YADDA AKE AMFANI

Jagoran Mai Amfani Mai Sauki Mataki-da-Mataki

Sigar 3.1.0 | Umarni Masu Saukin Fahimta
FARA AMFANI
Mene ne Business POS?
Business POS tsari ne mai sauki na kula da tallace-tallace da kayan kanti. Yana taimaka maka wajen:
  • Bibiyar kayayyakin da ke cikin kanti
  • Yin sayarwa ga kwastomomi cikin sauri
  • Buga takardar shaidar biya (receipt) kai tsaye
  • Ganin rahoton tallace-tallace na kullum
  • Kula da izinin ma'aikata
Yadda Ake Shiga (Login)
Mataki na 1: Jeka shafin yanar gizon POS dinka
Mataki na 2: Shigar da imel da kalmar sirri (password)
Mataki na 3: Danna maballin "Login"
Taimako: Kira 07026242926 idan kana bukatar taimako
Abubuwan da Kake Bukata
Abun BukataLallai Ne?
Kwamfuta, Tablet ko Wayar Hannu• Eh
Hadin Intanet• Eh
Google Chrome Browser• An Fi Bukata
Injin Buga Takarda (Printer)Zabinka ne
Kamara (Don sikanin Barcode)Zabinka ne
SHAWARA: Yi amfani da Google Chrome don tsarin yayi aiki yadda ya kamata. Kayi 'bookmark' na shafin don samun sa cikin sauri.
MATSAYIN MASU AMFANI
Matsayin Mai Gida/Admin
ADMIN - Yana da ikon sarrafa komai
  • Zai iya sakawa/gyarawa/goge kayayyaki
  • Zai iya bude wa ma'aikata 'account'
  • Zai iya ganin bayanan tsaro na kowa
  • Zai iya ganin duk wani rahoto
  • Zai iya canza tsarin duka manhajar
  • Zai iya lura da duk tallace-tallace
Matsayin Manaja
MANAJA - Yana da kusan dukkan ikon sarrafawa, banda na ma'aikata
  • Zai iya yin sayarwa
  • Zai iya canza farashi ko yawan kaya
  • Zai iya ganin duk wani rahoto
  • Zai iya buga 'barcodes'
  • Ba zai iya bude wa ma'aikata account ba
  • Ba zai iya ganin bayanan tsaro ba
Matsayin Akawu (Cashier)
CASHIER - Iyakarsa sayarwa kawai
  • Zai iya sayar wa kwastoma kaya
  • Zai iya amfani da sikanin barcode
  • Zai iya buga receipt
  • Ba zai iya canza bayanin kaya ba
  • Ba zai iya ganin rahotanni ba
  • Ba zai iya canza tsarin manhajar ba
MUHIMMI: Akawu (Cashier) iya sayarwa kawai zai iya yi. Ba zai iya canza farashin kaya ko ganin bayanan sirri na shagon ba.
YADDA AKE SAYARWA
Cikakken Tsarin Sayarwa
Bi wadannan matakai 6 masu sauki don yin sayarwa:
  1. Jeka Shafin Sales - Danna "Sales" a menu
  2. Saka Kaya a Kwando (Cart) - Akwai hanyoyi 3 na yin hakan
  3. Duba Kayan da ke Kwando - Tabbatar da yawa da farashinsu
  4. Danna "Complete Sale" - Idan komai ya kammala
  5. Saka Sunan Kwastoma - Rubuta sunansa ko "Walk-in"
  6. Buga/Dauko Receipt - Ka ba kwastoma takardarsa
SHAWARA: A koda yaushe ka tambayi sunan kwastoma. Receipt ya fi kyau idan akwai suna a jiki.
Hanyoyi 3 na Saka Kaya a Kwando
C

1. Amfani da Kamara (Mafi Sauri)

Yi amfani da kamara waya ko tablet don sikanin barcode

S

2. Amfani da Injin Sikanin (Scanner)

Saka lambar barcode ta hanyar amfani da injin sikanin

P

3. Danna Hoton Kaya (Mafi Sauki)

Danna hoton ko sunan kayan don sakawa a kwando

Umarnin Amfani da Kamara:
  1. Danna alamar kamara a shafin sayarwa
  2. Bada izinin amfani da kamara (Allow) idan an tambaye ka
  3. Nuna kamara kan lambar barcode
  4. Dakata na dakika 2
  5. Kayan zai shiga kwando kai tsaye
KULA DA KAYAYYAKI (INVENTORY)
Yadda ake Saka Sabbin Kayayyaki
Admin da Manaja ne kawai za su iya saka kaya:
  1. Danna "Inventory" a menu
  2. Danna maballin "Add Product"
  3. Cika wadannan bayanan guda 4:
    • Sunan Kaya (Product Name) - Abinda kwastomomi za su gani
    • Farashi (Price) - Farashin sayarwa a Naira
    • Yawa (Quantity) - Adadin da ke akwai a kanti
    • Barcode - Lambar sikanin (idan akwai)
  4. Danna "Add Product" don adanawa
Adadin Kaya - Jagoran Launuka
Adadin KayaLauniAbin yi
Kaya na nan (10+)• Kore (Green)Babu abin yi
Kaya ya fara karewa (5-9)• Ruwan Kwai (Orange)Siro wasu nan kusa
Kaya ya kusa karewa (1-4)• Ja (Red)Siro wasu yanzu-yanzu
Kaya ya kare (0)• Ja (Red)Ba za a iya sayarwa ba
Gyara Bayanin Kaya
Don canza bayanin wani kaya:
  1. Jeka shafin Inventory
  2. Nemo kayan a jerin sunaye
  3. Danna alamar fensir (pencil)
  4. Canza duk bayanin da kake so:
    • Sabunta farashi
    • Canza yawan kaya
    • Gyara sunan kaya
    • Saka ko canza barcode
  5. Danna "Update Product" don adanawa
LURA: Ana daukar rahoton duk wani gyara da aka yi. Admin zai iya ganin wanda ya yi gyara da kuma lokacin da aka yi.
Yaushe Ake Buga Sabon Barcode?
Buga barcode don:
  • Sabon kaya da ba shi da barcode
  • Kayan da lambar barcodensa ta baci
  • Idan injin sikanin ya kasa karanta tsohon code
  • Don samun tsari mai kyau a shago
TSARIN RECEIPT (TAKARDAR BIYA)
Bayan An Kammala Sayarwa - Me ke Faruwa?
Idan ka gama sayarwa:
  1. Tsarin zai nuna maka samfurin receipt din
  2. Receipt din yana dauke da:
    • Sunan shagonka da lambar waya
    • Kwanan wata, lokaci, da lambar receipt
    • Sunan akawu da na kwastoma
    • Duk kayayyaki da farashinsu
    • Jimillar kudin da za a biya
    • Sakon godiya
  3. Zabi abinda kake so:
    • Print Receipt - Don ba kwastoma
    • Download JPG - Don adanawa a waya/kwamfuta
    • Close - Don komawa sayarwa ta gaba
SHAWARA: A koda yaushe ka dauki hoton (JPG) receipt mai muhimmanci. Hakan zai sa ka kasance da kwafin sa idan takarda ta baci.
Nemo Tsofaffin Receipt
Kana bukatar buga tsohon receipt ko duba shi?
  1. Danna "Receipts" a menu
  2. Zaka ga dukkan tallace-tallacen da aka yi
  3. Nemo ta hanyar:
    • Sunan kwastoma
    • Kwanan watan da aka yi ciniki
    • Lambar receipt
  4. Danna "Download" don adanawa a matsayin hoto
  5. Danna "Reprint" don sake bugawa
Siffofin Receipt
SiffaAmfani
Lambar kansaKowane receipt yana da lambar sirri ta musamman
Sunan KwastomaYana nuna karramawa ga kwastoma
Bayanin KasuwanciBayanin shagonka na bayyana a kai
Bayanin KayaJerin abubuwan da aka saya a bayyane
Sauke JPGSamun kwafin ajiya a na'ura
RAHOTANNI DA NAZARI (REPORTS)
Rahotannin da ke Akwai
Admin da Manaja za su iya ganin:
  • Tallace-tallacen Yau - Abinda aka sayar yau
  • Rahoton Mako - Yadda aka yi kasuwanci a kwanaki 7
  • Rahoton Wata - Bayanan duk watan
  • Kayan da aka fi saya - Kayayyaki 10 na gaba-gaba
  • Kayan da ba su tafiya - Kayan da ba a cika saya ba
  • Kashe Kudin Kwastoma - Kwastomomin da suka fi siyan kaya
  • Rahoton Kaya - Yanayin kayan da ke akwai
Yadda ake ganin Rahotanni
  1. Danna "Reports" ko "Statistics"
  2. Zabi kalar rahoton da kake so
  3. Zabi kwanan wata (yau, mako, wata)
  4. Duba jadawali (charts) da lambobi
  5. Buga ko fitar da shi idan akwai bukata
Rahoton Tsaro (Admin Kadai)
Mai gida/Admin ne kawai zai iya ganin:
  • Duk Harkokin Tsarin - Wanene ya yi me
  • Canje-canjen Kaya - Gyaran farashi ko yawan kaya
  • Ayyukan Ma'aikata - Abinda ma'aikata suka yi
  • Bayanan Tallace-tallace - Duk cinikin da aka gama
  • Tarihin Gyara - Adadin gyaran da aka yi wa kaya
  • Sakon Tsaro - Abubuwan da ake shakka kansu
TSARO: Mai gida ne kawai zai iya ganin rahoton tsaro. Wannan na taimakawa wajen kauce wa zamba da bin diddigin canje-canje.
Fitar da Bayanai (Exporting)
Zaka iya fitar da:
  • Bayanin tallace-tallace zuwa Excel/CSV
  • Jerin kaya don duba stock
  • Tarihin receipt a matsayin fayiloli
  • Rahoton lissafin kudi (accounting)
SAITUNA DA GYARE-GYARE (SETTINGS)
Bayanin Shago
Admin zai iya saka bayanan shago:
  • Sunan Shago - Abinda zai fito a receipt
  • Adireshi - Inda shagon yake
  • Lambar Waya - Lambar tuntuba
  • Yanar Gizo - Shafin yanar gizo (idan akwai)
  • Sakon Receipt - Kalmar godiya
  • Logo - Hoton shagonka na receipt
Saitunan Kanka
Kowa zai iya canza:
D
Dark Mode - Canza launi zuwa fari ko baki

Yana taimaka wa idanu idan babu haske

P
Profile Dinka - Duba matsayinka da bayananka

Duba bayanan shigarka (login)

I
System Info - Sigar manhajar da yanayinta

Duba idan akwai sabuntawa (updates)

Saka Ma'aikaci (Admin Kadai)
Yadda ake saka sabon ma'aikaci:
  1. Danna "Staff" a menu
  2. Danna maballin "Add Staff"
  3. Cika bayanan ma'aikaci:
    • Suna da Mahaifa
    • Imel don shiga tsarin
    • Matsayi (Cashier/Manager/Admin)
    • Password (a kalla haruffa 6)
  4. Danna "Register Staff"
  5. Ka ba ma'aikaci bayanan shigarsa
DOKOKIN TSARO:
  • Kada ka taba bayyana password dinka
  • Kowane ma'aikaci ya kasance da account dinsa
  • A koda yaushe ka fita (logout) idan ka gama
  • Canza password akai-akai
Fita Daga Tsarin (Logging Out)
A koda yaushe kayi logout idan:
  • Zaka tafi ka bar kwamfutar
  • Lokacin tashi daga aiki ya yi
  • Zaka bar wani ya yi amfani da kwamfutar
  • Zaka tafi hutun dan lokaci
Don yin logout: Danna sunanka → Danna "Logout"
MATSALOLI DA MAGANINSU
Jagoran Magance Matsaloli
MatsalaMagani
Na kasa shiga (Login)Duba imel ko password. Tuntubi admin idan ka manta.
Ban ga kaya baDuba barcode dinka. Saka sabon kaya idan sabo ne.
Kamara ba ta sikaninBada izinin kamara a browser. Duba hasken wajen.
Tsarin yana nauyiDuba intanet dinka. Refresh shafin (F5).
Receipt ya ki buguwaDuba ko injin din a kunne yake kuma akwai takarda.
Bayanai ba su adanaDuba hadin intanet. Sake gwadawa.
Gajerun Hanyoyi na Keyboard
Sauke aiki da wadannan maballan:
  • F5 - Sabunta shafi (Refresh)
  • Ctrl + P - Buga shafin da kake kai
  • Tab - Matsawa tsakanin guraren rubutu
  • Enter - Tura bayanan da aka cika
  • Esc - Rufe abinda ya fito a fuska
Shawarwari ga Masu Wayar Hannu
Idan kana amfani da waya/tablet:
  • Kwantar da wayar (sideways) don gani sosai
  • Bada izinin kamara don yin sikanin
  • Saka shafin a matsayin 'shortcut' a fuskar waya
  • Yi amfani da Wi-Fi don sauri
  • Goge 'cache' na browser kowane wata